2 Satumba 2020 - 09:39
Sudan : Al' Bashir Ya Sake Gurfana Gaban Kotu

Hambararren shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al-Bashir ya sake gurfana gaban kotu don amsa tuhuma kan juyin mulkin Sojin da ya jagoranta a shekarar 1989.

ABNA24 : Yayin sauraren karar, Albashir wanda ke daure a gidan yarin Kober ya isa kotun tare da wasu mukarrabansa da suma ke fuskantar tuhuma, a zaman shari’ar na jiya wanda aka dage a watan jiya sakamakon hatsaniyar da ta tashi a harabar kotun.

Cikin watan Aprilun 2019 ne Sojoji suka hambarar da Omar al Bashir bayan zazzafar zanga-zangar kin jinin gwamnati da al’ummar kasar suka shafe watanni suna yi sakamakon tsadar rayuwa.

342/